Karamin Ministan Kiwon Lafiya da Jin daɗin Jama’a, Dakta Iziaq Adekunle Salako, ya bayyana cewa ’yan Najeriya miliyan 50 ke kamuwa da cututtuka sakamakon cin gurbataccen abinci.
Salako ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin, yayin bikin Ranar Abinci ta Duniya na 2026, mai taken “Daga kalubale zuwa Mafita – Ingantaccen Abinci a Ko’ina.”
A cewarsa, taken bikin na bana na tunatar da cewa samar da abinci wani muhimmin abin da ya shafi ci gaban ƙasa, lafiya, aiki da walwalar kowane ɗan Najeriya.
- NCDC ta tada hankali kan barazanar Ebola a Najeriya
- Najeriya ta fi kowace kasa yawan tamowa a 2025 —MSF
- Bincike: Rawar da sinadaran adana abinci ke takawa wajen yada cutar sankara
Ministan ya ce kwanaki kaɗan da suka gabata, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da sabon rahoto kan hasashen nauyin cututtukan da ake samu ta hanyar abinci daga shekarar 2000 zuwa 2021.
Ya ce sabon rahoton ya nuna cewa a duniya mutane sama da miliyan 8 ne ke kamuwa da cututtuka a kowacce shekara, yayin da sama da miliyan guda ke rasa rayukansu sakamakon gurbataccen Abinci.
Ministan Ya kara da cewa sama da kaso 80 cikin dari na mace macen mafi yawanci kananan yara ne yan kasa da shekaru 5.
A saboda haka Yayi gargadi game da yadda ake samun Sinadaran Dalma a cikin abinci da kuma wadda magungunan ajiya ke haifar wa a cikin nau’ikan Hatsi, kayan miya da kuma gurbataccen ruwa.
Ministan Yace ƙasar ta bullo da karin haraji kan abubuwan sha masu sukari, tare da tabbatar da tsarin sanya bayanai a jikin kwalin kayan abinci da aka sarrafa domin mai saye.
Wani rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO a shekarar 2025 ya nuna yadda Najeriyar ta tsallake mizanin da hukumar ta kafawa kasashe masu tasowa, wajen ganowa da dakile bullar cutattuka da ake samu daga gurbataccen abinci.
