Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan bashin kudade sama da Naira Biliyan 700 ga kananan’yan kwangila su 1,240, ke bin ta bashi.
Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Kasar Taiwo Oyedele ne ya bayyana amincewar, a ranar Litinin, kamar yadda Sakatariyar Yada Labaran sa Mary-Ann Duke, ta aikewa manema labarai.
Sanarwar tace biyan kudaden zai shafi ’yan kwangila ne da suka yi ayyuka a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a baya, kuma su ke bin tsohon bashin da bai zarce Naira Miliyan 100 ba.
Ma’aikatar Kudaden ta jaddada cewa za ta ci gaba da kiyaye tsarin tattalin arziki, yayin da take tabbatar da cewa an biya bashin, da nufin farfado da harkokin kasuwanci da kuma cicciba zagayawar kudade a cikin al’umma.
