Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas (Operation Haɗin Kai – OPHK) sun kuɓutar da wasu ƙarin mutum shida da aka yi garkuwa da su a yayin ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto a Jihar Borno.
Shafin muryar Najeriya ya ruwaito cewa waɗanda aka ceto sun haɗa da manya huɗu da jarirai biyu.
An kuɓutar da su ne a ƙauyen Talakawa da ke Ƙaramar Hukumar Chibok, bayan gudanar da hare-haren sama da na ƙasa bisa ingantattun bayanan sirri.
- Amnesty ta nemi a hukunta duk masu take haƙƙin ɗan adam a kudu maso gabas
- Haɗakar jami’an tsaro sun ƙwato shanu daga hannun ‘yan bindiga a Jihar Kogi
- Sojoji sun kashe mutane shida da ake zargin ’Yan ta’adda ne a Filato
A cewar OPHK, an yi garkuwa da mutanen ne a garin Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a watan Mayu.
An kai su zuwa wani wuri mai tsaro domin a duba lafiyarsu tare da ba su kulawar da ta dace.
Haka kuma, an ba su kayan agaji da sauran muhimman buƙatun yau da kullum, yayin da ake shirye-shiryen haɗa su da iyalansu cikin aminci.
Hedikwatar Rundunar ta ce dakaru na ci gaba da bibiyar ‘yan ta’addan da suka tsere.
Ta kuma bayyana cewa an ƙwato harsasai 50 na bindigar PKT a hanyar da maharan suka bi yayin janyewa.
OPHK ta buƙaci al’umma su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, su rika kai rahoton duk wani motsi da ke tayar da hankali ga hukumomin tsaro, sannan su guji yaɗa ko amincewa da bayanan da ba a tabbatar da sahihancin su ba.