Rundunar Operation ENDURING PEACE ta ce dakarunta sun kashe aƙalla mutane shida da ake zargin ’yan ta’adda ne, tare da ƙwato bindigogi ƙirar gida a wasu hare-hare da suka kai a sassa daban-daban na Jihar Filato.

Rundunar ta kuma ce dakarunta sun daƙile wani yunkurin kai hari kan Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun Operation ENDURING PEACE, Chinonso Oteh, ya bayyana a ranar Alhamis cewa an gudanar da hare-haren ne tsakanin ranar 26 ga Yuni zuwa 2 ga Yuli a ƙananan hukumomin Jos ta Kudu da Barkin Ladi.

Ya ce an gudanar da waɗannan hare-haren ne bayan samun sahihan bayanan sirri game da wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke aiki a yankin da rundunar ke gudanar da ayyukanta.

A cewarsa, dakarun Sashe na 6 (Sector 6) sun kai samame a yankin Gero Highground da ke Jos ta Kudu a ranar 26 ga Yuni, bayan rahotannin da ke nuna cewa waɗanda ake zargin ’yan ta’addane suna aikata munanan laifuka a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *