Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, NFF, ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan ƙaddamar da Cibiyar Yaƙi da Miyagun ƙwayoyi a Wasanni ta Najeriya, NADC, da aka yi a ranar Alhamis.
Wannan ya biyo bayan sanya hannu kan dokar yaƙi da miyagun kwayoyi ta ƙasa ta 2025, wadda ta kafa cibiyar a matsayin hukuma bisa doka da aka ba ta wajibcin yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya da kuma bin ƙa’idojin da sauran kasashen duniya ke bi.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan yada labaran Hukumar NFF, Olajire Pius, ya aike wa gidan Rediyon Blueprint ranar Jumma’a.
A cewar sanarwar, babban sakataren NFF, Dokta Mohammed Sanusi, ya ce wannan mataki ya ƙara nuna jajircewar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kai wasannin Najeriya ga matsayi mafi kyau, da kuma niyyar tabbatar da gaskiya da aminci a duk wasannin da Najeriya ke takara a matakin duniya.
- Gwamati ta san da labarin hukumar bogi-Mataimakin Shugaban ƙasa na musammam
- Burkina Faso da Mali da Nijar sun fara Shirin fita daga ICC
- Amnesty International ta yi Allah wadai da ƙaruwar ɗaukar doka a hannu a Arewacin Najeriya
- Jami’ar jin ƙai ta raba rigu
“Keta dokar shan miyagun ƙwayoyi a tsawon shekaru bai yiwa martabar ƙasar mu kyau ba. Tabbas, hukumar NADC za ta tabbatar da adalci a wannan fannin tare da mayar da martabar ƙasarmu a matsayin al’umma da ba ta amince da shan miyagun kwayoyi kwata-kwata.”
Sanusi ya kuma taya Sakataren Zartarwa harwayau kuma Shugaban Hukumar NADC, Alhaji Mainasara Illo, murnar naɗin sa, yana mai cewa NFF na da cikakken ƙwarin gwiwa kan ƙwarewarsa na jagorantar cibiyar zuwa ga nasara.
“Mun yi imani cewa zai gudanar da aikin da mai girma shugaban ƙasa ya daura mishi.”
Illo, wanda fitaccen mai watsa shirye-shirye ne, ya kasance mataimakin shugaban shirya gasar (All-Africa Games) ta 8 da Najeriya ta karɓi baƙunci a shekarar 2003, sannan ya kasance shugaban shirya gasar cin kofin duniya ta ‘yan ƙasa da shekara 17 ta FIFA da aka gudanar a Najeriya a shekarar 2009.
Kazalika, Hukumar NFF ta kuma taya likitan tawagar Super Eagles, Dokta Ibrahim Gyaran, murna kan naɗin sa a matsayin mamba a Cibiyar Yaki da Miyagun ƙwayoyi ta Najeriya.