Ƙungiyar Amnesty International ta Najeriya ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin ƙaruwar ɗaukar doka a hannu a wasu sassan Arewacin Najeriya, tana mai cewa hakan na barazana ga bin doka da oda.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta yi nuni da lamarin da ya faru a ranar Laraba 1 ga Yulin 2026 a unguwar Kofar Soro da ke birnin Katsina, inda ta ce taron yara da matasa dauke da makamai suka kewaye kotu suna neman a kashe wani mutum da ake yi wa shari’a kan zargin yin saɓo ga addini, ba tare da bin tsarin shari’a ba.
Amnesty ta kuma ambaci kisan Ummulkhairi, wata malama kuma uwa mai ‘ya’ya biyar da aka ƙone a Mararabar Jos da ke jihar Kaduna, sakamakon zargin da ƙungiyar ta ce ba a tabbatar ba na yunƙurin sace yara, lamarin da ya faru kimanin kwanaki goma kafin abin da ya faru a Katsina.
- Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen dala biliyan 1.25
- Tinubu ya amince da ayyukan tituna 27 na Naira tiriliyan 3.9 a jihohi 15
Ƙungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare na nuna ƙara samun rashin bin doka da kuma raina tsarin shari’a, tana mai jaddada cewa duk wanda ake zargi da aikata wani laifi yana da haƙƙin samun adalci ta hanyar shari’a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Amnesty International ta buƙaci gwamnatin jihar Katsina da hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da gurfanar da duk wanda ake zargi da tayar da tarzoma ko ɗaukar doka a hannu, tana mai cewa adalci na gaskiya yana samuwa ne ta hanyar bin doka, ba ta hanyar tashin hankali ko hukuncin taron jama’a ba.