Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen dala biliyan 1.25 a ƙarƙashin shirin gwamnatin Najeriya na bunƙasa zuba jari da ƙara samar da ayyukan yi (NAIJA).
Bankin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar tare da ƙaddamar da sabon tsarin haɗin gwiwa da Najeriya na shekarun 2026 zuwa 2032.
A cewar bankin, sabon tsarin zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ta hanyar bunƙasa saka hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu da kuma ƙarfafa ci gaban tattalin arziki.
- Dillalan Man Fetur sun yi barazanar rufe gidajen mai idan…
- Arewa bata taba samun masoyi kamar Tinubu ba-Uba Sani
- Tinubu ya amince da ayyukan tituna 27 na Naira tiriliyan 3.9 a jihohi 15
Bankin ya ce wannan sabon rancen zai taimaka wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka haɗa da bunƙasa kasuwannin hannayen jari, da inganta dokokin tattalin arziki na zamani da na gwamnati ta yanar gizo, da faɗaɗa samar da wutar lantarki, da rage shingayen kasuwanci tsakanin ƙasashen ECOWAS da yankin ciniki na AfCFTA, da inganta iri na noma da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati.
Haka kuma, sabon tsarin haɗin gwiwar zai samar da wutar lantarki ga mutum miliyan 32, da haɗa mutum miliyan 58 da intanet, da inganta harkokin lafiya da abinci mai gina jiki ga mutum miliyan 40, tare da tallafa wa manoma miliyan 9.5 domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa jarin ɗan Adam.
Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya ce manufar ita ce a tabbatar sauye-sauyen tattalin arzikin da aka samu sun haifar da ingantuwar rayuwar al’umma ta hanyar samar da ayyukan yi da jawo ƙarin masu zuba jari.