Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Mai shari’a Musa Liman, a hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, ya kuma yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar yana ƙalubalantar naɗin David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaban ƙasa da sakataren ƙasa na jam’iyyar, yana mai cewa ƙarar ba ta da tushe.
Mai shari’ar ya amince da ƙorafe-ƙorafen farko da jam’iyyar ADC da tsohon shugabanta Ralph Nwosu, da David Mark da Aregbesola suka gabatar, waɗanda suka nemi kotun ta yi watsi da ƙarar Abejide.
Kotun ta ce ba ta da hurumin shiga cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa, saboda batun da aka gabatar ba ya cikin waɗanda kotu ke da ikon yanke hukunci a kansu.
- Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen dala biliyan 1.25
- Belgium ta kori Senegal daga Gasar Kofin Duniya
- CBN ta soke lasisin bankunan Microfinance 46, NDIC ta fara biyan masu ajiya
Haka kuma, Mai shari’a Liman ya ce Abejide bai nuna cewa an tauye masa wata haƙƙi ta doka sakamakon zuwan shugabancin David Mark ba, don haka bai da cikakken ikon shigar da irin wannan ƙara.
Kotun ta kuma ce Abejide, wanda mamba ne na Majalisar Wakilai, bai fara amfani da hanyoyin sasanta rikici na cikin jam’iyyar kafin ya garzaya kotu ba.
Mai shari’ar ya warware dukkan batutuwan da ke cikin ƙarar ne a madadin waɗanda ake ƙara.
Dangane da batun ko David Mark, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, da Rauf Aregbesola, tsohon Gwamnan Jihar Osun, sun zama shugabannin jam’iyyar bisa tanadin doka, kotun ta yanke hukuncin cewa sun bi ƙa’ida, tare da yin watsi da hujjojin mai ƙara.
Kotun ta ce miƙa shugabancin jam’iyyar daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.
Mai shari’ar ya kuma amince cewa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 2 ga Yulin 2025 ya kasance share fage ne ga taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka yi ranar 29 ga Yulin 2025, wanda a cikinsa aka zaɓi David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugabannin jam’iyyar, kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ido kan taron.
Saboda haka, kotun ta bayyana cewa zaɓen David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugabannin ADC ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, dokokin zaɓe da sauran tanade-tanaden doka.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Abejide ya shigar da ƙarar ne domin dakatar da shugabancin David Mark a jam’iyyar ADC.
A cikin takardar ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1637/2025, wadda aka shigar ranar 15 ga Fabrairu, ɗan majalisar ya shigar da ƙara kan jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, David Mark, Rauf Aregbesola da kuma INEC.
AN ta kuma bayyana cewa Ralph Nwosu shi ne tsohon shugaban jam’iyyar ADC wanda ya sauka daga mukaminsa domin bai wa David Mark damar jagorantar jam’iyyar.