Hukumar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta soke lasisin gudanar da harkokin banki na bankunan Microfinance guda 46, yayin da ta naɗa Hukumar Kare Asusun Masu Ajiya ta Najeriya (NDIC) a matsayin mai kula da rushewa da rufe bankunan bisa tanadin dokokin BOFIA ta 2020 da Dokar NDIC ta 2023.
A cikin wata sanarwa da NDIC ta fitar, ta ce daga ranar 1 ga Yulin 2026 bankunan da abin ya shafa ba su da izinin ci gaba da gudanar da harkokin banki a Najeriya.
Hukumar ta yi gargaɗi ga jama’a da su guji yin kowace irin mu’amala da bankunan, tare da jan kunnen duk wanda zai yi yunƙurin ɓoye, kwashe ko lalata kadarori da takardun bankunan cewa hakan ya saɓa wa doka kuma zai iya jawo hukunci.
- CBN ta soke lasisin bankunan Microfinance 46, NDIC ta fara biyan masu ajiya
- INEC da NOA sun haɗa gwiwar wayar da kan jama’a gabanin zaɓen 2027
- A daina kai hare-hare kan addinin Musulunci da Musulmai a Najeriya-NSCIA
NDIC ta bayyana cewa ta riga ta fara karɓe da rufe bankunan cikin tsari, tare da tantance bayanan masu ajiya domin fara biyan waɗanda suka cancanci karɓar kuɗaɗensu da dokar inshorar ajiya ta tanada.
Hukumar ta kuma tabbatar wa masu ajiya da sauran jama’a cewa za ta ci gaba da sanar da su matakan da ake ɗauka yayin da aikin rushewa da biyan haƙƙin masu ajiya ke gudana.