Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta Janar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan Najeriya.

Hakan ƙunshe ne cikin wata sanar wa da Abbas Jimoh, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya fitar a madadin ta.

Sanarawar ta nuna cewa wannan ƙuduri ne ya sa majalisar ke nuna haƙuri da kauce wa mayar da martani duk da abin da ta bayyana a matsayin tsokana, cin zarafi da kuma zargin Musulunci da Musulmai ba tare da hujja ba. Majalisar ta ce ya kamata a fahimci cewa haƙuri ba yana nufin tsoro ko rauni ba ne, amma komai yana da iyaka.

Majalisar ta ce, duk da cewa a fili yake Musulmai na fuskantar nuna wariya a wasu fannoni na rayuwar jama’a a Najeriya, abin mamaki ne yadda har yanzu akwai wasu da ke zargin Musulmai da zalunci da tsananta wa wasu.

A cewarta, wasu ƙungiyoyin ƙetare na amfani da irin waɗannan zarge-zarge domin tayar da rikici, haddasa rashin zaman lafiya da kuma raunana ƙasar.

NSCIA ta yi nuni da wasu kalamai da tsohon shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ya yi a wani shirin talabijin na Channels Television, inda ya ce kashi 90 zuwa 95 cikin 100 na masu aikata laifuffuka Musulmai ne.

Majalisar ta bayyana wannan furuci a matsayin marar tushe, rashin gaskiya da kuma rashin ɗa’a, tana mai cewa ya kamata gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su ɗauki mataki.

Ta ce irin waɗannan kalamai sun kamata su jawo aƙalla tsawatawa daga hukumomin da ke kula da kafafen yaɗa labarai domin kare zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Majalisar ta kuma zargi kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro da yin watsi da irin waɗannan kalamai, duk da cewa suna iya jawo martani da zai iya barazana ga zaman lafiyar ƙasa. Ta ce da ace wani shugaban Musulmi ne ya yi irin wannan furuci, da tuni hukumomin tsaro sun gayyace shi domin amsa tambayoyi.

Har ila yau, NSCIA ta ce wasu shugabannin Kiristoci na zargin Fulani—waɗanda, a cewarta, ake nufi da Musulmai—da hannu a sace-sacen mutane da suka faru a Jihar Oyo. Amma ta ce wanda aka kama dangane da wani lamarin garkuwa da mutane a Ibadan ba Musulmi ba ne, illa ma fasto ne.

ya yi korafi kan abin da ake kira tikitin Kirista da Kirista. Ta ce a yau ana amfani da wannan batu wajen hana Musulmai haƙƙoƙinsu na siyasa.

A ƙarshe, NSCIA ta ce tana ci gaba da kira ga Musulmai da su yi haƙuri, amma ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan da suka dace kafin haƙurin Musulmai ya ƙare, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da kai hare-hare da nuna wariya a kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *