Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ya karɓi baƙuncin Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, tare da tawagarsa a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Ziyarar ta bai wa hukumomin biyu damar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan harkokin ƙasa, ilmantar da masu zaɓe da kuma bunƙasa ƙimar dimokuraɗiyya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Da yake maraba da tawagar NOA, Farfesa Amupitan ya bayyana cewa ganawar ba ziyarar girmamawa kawai ba ce, illa wata muhimmiyar tattaunawa tsakanin hukumomi biyu da kundin tsarin mulki ya ɗora wa nauyin wayar da kan ‘yan Najeriya da kuma ƙarfafa al’adun dimokuraɗiyya.

Ya ce: “INEC ba za ta iya gina ingantacciyar dimokuraɗiyya ita kaɗai ba. Za mu iya sayen mafi ingancin na’urorin BVAS, mu inganta tsarin duba sakamakon zaɓe na IReV, tare da kyautata tsarin gudanar da zaɓe. Amma duk waɗannan ba za su yi wani amfani ba idan har ‘yan ƙasa ba su fahimci muhimmancin ƙur’unsu ba ko kuma ba su shiga harkokin dimokuraɗiyya yadda ya kamata.”

Farfesa Amupitan ya ce bunƙasar dimokuraɗiyyar Najeriya ba za ta samu ne ta hanyar inganta fasahar gudanar da zaɓe kawai ba, yana mai jaddada cewa dole ne ‘yan ƙasa su kasance masu cikakken bayani kuma su taka rawa a tsarin dimokuraɗiyya.

Shugaban INEC ya bayyana NOA a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa saboda kasancewarta a matakin al’umma da kuma ikon da take da shi na isar da saƙo kai tsaye ga jama’a a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce manyan ƙalubalen da ake fuskanta sun haɗa da ƙarancin fitowar masu zaɓe, yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma rashin fahimtar tsarin zaɓe, yana mai cewa waɗannan matsaloli na buƙatar haɗin gwiwar hukumomin biyu domin magance su.

Tun da farko, Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya gode wa shugaban INEC, kwamishinoni, daraktoci da ma’aikatan hukumar bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ƙarfafa tsarin zaɓe a Najeriya.

Ya ce: “Dimokuraɗiyya ita ce ginshiƙin da rayuwar wannan ƙasa ke dogaro da shi. Haƙƙin ‘yan ƙasa na zaɓar shugabanninsu abu ne da ya wajaba mu kare tare da bunƙasa.”

Issa-Onilu ya yaba wa INEC saboda fahimtar muhimmancin wayar da kan masu zaɓe, yana mai cewa yawaitar matasa a Najeriya ya sa ci gaba da ilmantar da jama’a kan dimokuraɗiyya ya zama wajibi fiye da kowane lokaci.

Ya bayyana cewa kasancewar NOA tana da ofisoshi a faɗin ƙasar, hakan na ba ta damar isa kai tsaye ga al’ummomi ta hanyar haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, kasuwanni, ƙungiyoyin direbobi, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki.

A ƙarshe, shugaban NOA ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sashen wayar da kan masu zaɓe na INEC da sashen Ilimin Ɗabi’u da Dimokuraɗiyya na NOA domin ƙara yawan fitowar jama’a zaɓe, yaƙi da yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *