Shagunan da aka lalata da kuma tarkacen kayan da aka watsar ne suka rage a cikin wasu shaguna kusa da birnin tashar jiragen ruwa na Durban a ranar Laraba, bayan fasa shaguna a lokacin zanga-zangar da ke neman a kori baƙi da ba su da takardun izini daga Afirka ta Kudu.

Dubban mutane ne suka yi tattaki a fadin ƙasar a ranar Talata bayan wani shiri na tsawon makonni da wasu ƙungiyoyi  suka jagoranta, suna neman a kori baƙi marasa izini kafin 30 ga Yuni, abin da  ya sa dubban mutane suka tsere.

‘Yan sanda sun tura jami’ansu cikin shirin gaggawa domin kula da zanga-zangar, inda suka sanar a ranar Laraba cewa yawancin zanga-zangar ta kasance cikin lumana, amma an kama kusan mutane 900, wasu daga cikinsu saboda fasa shaguna.

An kiyasta cewa asarar da aka yi ta kai miliyoyin rand, inda ‘yan kasuwa suka ce ba su da tabbacin ko za su sake buɗe shagunan nasu.

Mohamed Abdul, mai shekaru 29, ya ce wata babbar ƙungiyar masu zanga-zanga ta kutsa cikin shagonsa dake sayar da abinci da kayan gini da tufafi da misalin ƙarfe 6:00 na yamma ranar Talata.

Abdul, wanda ya fito daga Somaliya, ya ce ya shafe shekaru 11 yana zaune a yankin a bisa doka shi ba baƙo bane.

“Al’umma sun san ni, kuma wannan na ɗaya daga manyan shagunan da mutane ke dogaro da shi, kuma muna taimaka wa iyalan da ba su da komai.”

Ya ce maharan har sun kwashe na’urar ATM da ke cikin babban shagon, amma aka bar akwatin ajiyar kuɗi a waje.

Wannan shi ne karo na farko da aka shirya zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a cikin wani shiri na tsawon makonni na adawa da baƙi marasa izini, inda masu zanga-zanga ke zargin suna kwace musu ayyuka.

Wata hukumar tsaro ta gwamnati ta ce an gudanar da tattaki 120 a fadin ƙasar a ranar Talata, kuma 12 ne kawai suka bukaci shigar jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *