Gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaddamar da cibiyar inganta ruwa da tsaftar muhalli domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma faɗaɗa samar da tsaftataccen ruwan sha da ingantattun ayyukan tsafta ga al’ummomin karkara.

Mukaddashin Shugaban Cibiyar Kula da Lafiyar Jama’a da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NIPHID), Dakta Dalhatu Aminu, ya ce adawar da Hukumar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) da wasu ƙungiyoyi suka nuna kan kudirin dokar kafa cibiyar ta samo asali ne daga rashin fahimtar abin da kudirin ya ƙunsa.

Ya ce kudirin, wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen ya ɗauki nauyi, ba ya ƙirƙirar wata hukuma da za ta maye gurbin ko ta maimaita ayyukan NCDC.

A cewar sa, manufar cibiyar ita ce kula da marasa lafiya, horas da ƙwararru da gudanar da bincike kan cututtuka masu yaɗuwa, tare da taimakawa NCDC ba tare da katsalandan ga aikinta ba.

Dakta Aminu ya ce kudirin ya tanadi a fili cewa cibiyar ba za ta shiga ayyukan sa ido kan barkewar cututtuka ko jagorantar martanin ƙasa ga annoba ba, sai dai ta yi aiki tare da NCDC wajen bincike, horo da tallafawa idan an buƙaci hakan.

Sai dai Darakta Janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ya taɓa bayyana wa Majalisar Wakilai cewa wasu sassan kudirin na iya maimaita ayyukan da dokar NCDC ta tanada, lamarin da zai iya haifar da rikici tsakanin hukumomi da raunana tsarin daƙile barkewar cututtuka.

Amma Dakta Aminu ya ƙalubalanci wannan ra’ayi, yana mai kira ga NCDC da sauran masu adawa da su sake nazarin sahihin kudirin dokar, su kuma shiga tattaunawa domin magance duk wata damuwa ta gaskiya.

Ya jaddada cewa Najeriya na buƙatar NCDC tare da cibiyoyin bincike da horaswa domin su riƙa tallafa wa juna wajen inganta tsaron lafiyar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *