Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 11 da kuma shugabannin yankunan ci gaban ƙananan hukumomi 13, wato LCDAs, inda ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da riƙon amana da dalci da kuma tsoron Allah.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana da gaskiya da adalci yana mai cewa sakamakon ya nuna irin amincewar da al’ummar jihar suke da ita ga jam’iyyar APC da kuma manufofin gwamnatinsa na ci gaba.

Gwamnan ya ce ƙananan hukumomi su ne ginshiƙin dimokuraɗiyya, domin su ne ke da alhakin isar da ayyukan gwamnati zuwa ga al’umma, ƙarfafa haɗin kan jama’a da kuma inganta tsaro a matakin ƙasa.

Inuwa Yahaya ya kuma sake jaddada cewa tsarin ƙirƙirar LCDAs zai ci gaba  yana mai bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar domin ƙarfafa mulki da ci gaba a matakin ƙananan hukumomi.

Gwamnan na Jihar Gombe  ya ce saboda ingantaccen tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati da kuma kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Ayyukan Ci Gaba ta Ƙananan Hukumomi, wato JPDA, ƙananan hukumomin jihar sun samu ƙarin ƙarfin tattalin arziki da zai ba su damar gudanar da ayyukan raya al’umma yadda ya kamata.

Ya kuma buƙaci sabbin shugabannin da su kasance masu sauraron koke-koken jama’a da masu gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa duk wata shawarar da za su ɗauka za ta kasance domin amfanin al’umma baki ɗaya, ba wai don biyan buƙatun kansu ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *