An gina cibiyar tare da tanadar mata kayan aiki

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar kula da cututtukan koda da kuma makarantar koyar da fasahar kiwon lafiya a garin Hadejia da ke Jihar Jigawa.

An gina cibiyar ne tare da tanadar  da kayan aikin da ake buƙata, kuma an sanya wa Asibitin suna Oluremi Tinubu domin girmama gudummawar Uwargidan Shugaban Ƙasa wajen tallafa wa al’ummomin da ba su da isassun cibiyoyin lafiya.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta kuma kafa Makarantar Bola Ahmed Tinubu ta hannun Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Bayanai ta Ƙasa,(NITDA) domin horas da matasa da ma’aikatan lafiya kan yadda za a yi amfani da fasaha wajen magance matsalolin kiwon lafiya.

Da take jawabi yayin ƙaddamar da cibiyoyin, Oluremi Tinubu ta ce an kafa su ne domin gano cututtukan koda da wuri tare da dakile su kafin su tsananta, musamman ga marasa galihu.

Ta ce lafiya ita ce ginshiƙin rayuwa, kuma rigakafi da gano cuta da wuri na taimakawa wajen ceton rayuka. Ta kuma bayyana cewa cibiyar da makarantar za su yi aiki tare wajen samar da sabbin hanyoyin amfani da fasaha domin yaƙi da cututtukan koda.

Shi ma Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa, ya bayyana makarantar a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa amfani da fasaha wajen inganta harkokin kiwon lafiya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *