An katse wasan Novak Djokovic da Yibing Wu a filin wasa na (Centre Court) a gasar Wimbledon yayinda wani mai kallo ya mika bukatar auren budurwarsa, Kuma bayan tace “eh” ga zoben, Djokovic ya nemi a gayyace shi bikin auren.
Djokovic dan kasar Serbia, ya daga wa yan kallo alamar yatsa a sama, yana fadin “Ina so a gayyace ni bikin auren nan.”
Daga bisani Djokovic, ya yi alamar zuciya da yatsun sa, yayin da dandazon yan kallo a filin wasan na Centre Court ke bayyana farin ciki.
- Moroko ta doke Holand don kaiwa matakin ƙungiyoyi 16 a bugun fanareti
- Brazil ta tsallake rijiya da baya karawarsu da Japan
Mutumin, mai doguwar gashin kai mai lankwasa, riga mai shuɗi da gilashin shuɗi, ya durƙusa da gwiwa ɗaya ya yi tambayar.
Budurwarsa, mai sanye da rigar da ke da launin fari, shuɗi da rawaya, tare da gilashin rana mai ruwan hoda, ta amince cikin farin ciki yayin da suka kalli Djokovic suka nuna masa alamar yatsa a sama.
