Da ƙyar da jiɓin goshi, Brazil ta  samu gurbin zuwa matakin ƙungiyoyi 16 na Gasar Cin Kofin Duniya bayan Gabriel Martinelli ya zura ƙwallo a mintin ƙarin lokaci.

Hakan ne kuwa ya tabbatar wa da Brazil ɗin nasara mai ban mamaki da ci 2-1 akan Japan. 

Ƙasar Japan ce ta fara zura ƙwallo a ragar Brazil a rabin lokacin farko, ta hannun Kaishu Sano.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci Brazil ta kara inganta salon wasanta, inda Casemiro ya farke ƙwallon da aka ci su a karon farko.

Shigowar ɗan wasan Arsenal Gabriel Martinelli daga benci ke da wuya ya ci ƙwallar da ta bai wa Brazil nasara a minti na 95, inda hakan ya faranta wa magoya baya rai a filin wasa na Houston.

Casemiro mai shekaru 34 da kwanaki 126, shi ne ɗan Brazil na biyu mafi tsufa da ya ci ƙwallo a Gasar Cin Kofin Duniya, bayan Bebeto kawai a 1998 (shekaru 34 da kwanaki 137 akan Denmark).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *