Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya ce samun tabbataccen tsarin dokoki, da daidaito da kuma gaskiya a fannin man fetur na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa gwiwar masu zuba jari a Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a wajen buɗe Taron Manyan Lauyoyi da Mashawartan Shari’a na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja, inda ya yaba wa Hukumar NMDPRA bisa samar da dandalin tattaunawa tsakanin hukumomin da ke sa ido da kamfanonin da ke gudanar da harkokin man fetur.
- Matatar Ɗangote ta fara shigo da ɗanyen mai daga UAE
- Najeriya ta cika shekara 20 ba tare da ƙidayar Jama’a ba
Lokpobiri ya ce aiwatar da Dokar Masana’antar Man Fetur ta shekarar 2021 da kuma sassauta dokokin kasuwar man fetur sun taimaka wajen ƙara ƙarfin tace mai a cikin ƙasa, da inganta wadataccen man fetur da kuma samar da sabbin hanyoyin zuba jari.
Ya kuma buƙaci mashawartan shari’a su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen inganta shugabanci, da ƙarfafa zuba jari cikin gaskiya da kuma bunƙasa masana’antar man fetur a Nijeriya.