Rundunar sojin Operation Hadin Kai ta ce ta ceto ɗalibai da malamai 10 da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka sace a wani hari da suka kai makarantar sakandaren fasaha ta Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba a Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa, mukaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safiyar ranar Litinin, lokacin da mayaƙan suka kai hari makarantar yayin da ɗalibai ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO.

Sanarwar ta ce nan take rundunar ta tura sojoji tare da jiragen yaƙi domin gudanar da aikin ceto. Bayan artabu da mayaƙan a yankin Daggu, sojojin sun samu nasarar ceto mutum 10 ba tare da sun ji rauni ba.

Rundunar ta ce har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin ceto mutum guda da ya rage, tare da neman waɗanda suka kai harin domin kama su da gurfanar da su a gaban shari’a. Ta kuma bayyana cewa sojojin sun kashe wasu daga cikin mayaƙan tare da ƙwace babura bakwai da suka yi amfani da su wajen kai harin.

Sai dai sanarwar ta tabbatar da cewa wani soja da kuma ɗaya daga cikin jami’an sa kai na JTF sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da mayaƙan.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *