Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Kula da Harkokin Mai ta NMDPRA, Mallam Rabiu Abdullahi Umar, ya ce manufar hukumar ba bin doka kaɗai ba ne, har ma da samar da yanayi mai kyau da zai ƙarfafa amincewar masu zuba jari.
Ya bayyana haka a wajen Taron Manyan Lauyoyi da Mashawartan Shari’a na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce taron ya zama wata muhimmiyar hanya ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumar da kamfanonin da ke da lasisin gudanar da harkokin man fetur.
- Najeriya ta cika shekara 20 ba tare da ƙidayar Jama’a ba
- Matatar Ɗangote ta fara shigo da ɗanyen mai daga UAE
Shi kuma Mashawarcin Shari’a na hukumar, Dr. Joseph Tolorunse, ya ce bin doka shi ne ginshiƙin tsarin sa ido, amma babban buri shi ne samar da yanayin da masu zuba jari za su samu tabbacin gudanar da kasuwanci cikin adalci, da gaskiya da daidaito.
Ya ƙara da cewa hakan ne zai taimaka wajen gina masana’antar man fetur mai ƙarfi, da gasa da kuma jan hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.