Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta mayar wa ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, belinsa tare da ba shi sabon beli na Naira miliyan 200.
Mai shari’a Muhammad Umar ya yanke hukuncin ne a ranar Talata, inda ya ce Sowore zai gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa kafin a bashi belin.
Kotun ta ce ɗaya daga cikin masu tsaya masa dole ne ya kasance sarki ko shugaban gargajiya daga garinsu, yayin da na biyun kuma dole ne ya mallaki kadara a Babban Birnin Tarayya Abuja.
- EFCC ta ƙwato sama da Naira biliyan 38 a binciken kuɗaɗen gyaran matatun mai
- NDC ta sake samun damar amfani da shafin INEC
- Moroko ta doke Holand don kaiwa matakin ƙungiyoyi 16 a bugun fanareti
Kotun ta kuma umarci Sowore da ya miƙa fasfot ɗinsa ga magatakardar kotu har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.
Ana tuhumarsa ne kan laifuffuka biyar da suka shafi zargin aikata laifukan yanar gizo, bayan wani furuci da ya yi kan Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
A ranar 16 ga watan Yuni ne kotun ta soke belinsa tare da bayar da sammacin kama shi, bayan da ya gaza halartar zaman kotu.
Daga bisani ya miƙa kansa ga kotun a ranar 22 ga watan Yuni, inda ya nemi a janye Mai shari’ar daga shari’ar, amma kotun ta yi watsi da buƙatar tare da tsare shi a Gidan Gyaran Hali na Kuje.
Sai dai a zaman kotun na ranar Talata, Mai shari’a Muhammad Umar ya amince da sabuwar buƙatar belin Sowore, tare da mayar masa da belinsa bisa sharuɗɗan da kotun ta gindaya.