Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), Ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince da aiwatar da manyan sauye-sauye ga shirin yi wa ƙasa hidima na matasa, wato NYSC, karo na farko tun bayan kafuwarsa a shekara ta 1973.
Daga cikin muhimman sauye-sauyen akwai maye gurbin shugaban NYSC mai mukamin soja da Darakta Janar farar hula, da kuma sake fasalin shirin hidimar ƙasa zuwa rassa guda 11 da za su mayar da hankali kan koyar da sana’o’i da bunƙasa kwarewar matasa haka gwamnatin ta amince da sake fasalin shirin sansanin horaswa inda za a tsawaita lokacin horo daga makonni uku zuwa makonni shida.
Har ila yau, an sauya tsarin kayan sawa na masu yi wa ƙasa hidima, an kuma ba da umarnin gyara dokar shirin domin waɗanan sauye-sauye su samu cikakken tushe na doka.
Ministan Matasa Ayodele Wisdom, ya ce an fara aikin duba tsarin NYSC ne tu
- Oluremi Tinubu ta ƙaddamar da cibiyar kula da cututtukan koda da makarantar fasahar lafiya a Jigawa
- Mai kallon gasar Wimbledon ya mika bukatar aure ga budurwar sa ana tsaka da wasa
n shekara ta 2025 bayan kafa kwamitin da ya yi nazari kan yadda za a sabunta shirin domin ya dace da bukatun Najeriya na wannan zamani.
Ya bayyana cewa, duk da irin rawar da NYSC ta taka wajen haɗa kan ‘yan Najeriya bayan yaƙin basasa, yanzu lokaci ya yi da za a mayar da hankali wajen samar wa matasa ƙwarewa da ayyukan yi da kuma ƙara habaka tattalin arzikin ƙasa.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan manufofi da tsare-tsare, Hadiza Bala Usman, ta ce wannan shi ne garambawul mafi girma da aka taɓa yi wa NYSC cikin shekaru 53 da kafuwarta.
Ta ƙara da cewa, manufar sauye-sauyen ita ce mayar da NYSC wata hukuma ta farar hula da za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ƙwarewar matasa, samar da ayyukan yi da kuma taimakawa gwamnatin tarayya wajen cimma burinta na gina tattalin arzikin Najeriya mai darajar dala tiriliyan ɗaya .