Trump ya umarci gidajen sayar da mai su rage farashin fetur nan take

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya umarci gidajen sayar da mai a faɗin ƙasar da su rage farashin fetur nan take domin jama’a su amfana da faɗuwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na yanar gizo, inda ya zargi masu sayar da mai da ci gaba da tsayar da farashi mai duk da cewa farashin gangar danyen mai ya ragu.

Yana mai gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da cin zarafin masu amfani da man fetur ba, ta hanyar ƙarin farashi.

Trump ya ce ya kamata farashin man fetur ya ragu zuwa kusan dala 2.50 kan kowane galan, domin Amurkawa su amfana da saukar farashin danyen mai a duniya.

Rahoton ya ce wannan mataki na Trump ya yi daidai da umarnin da Heineken Lokpobiri ya bai wa masu kasuwar mai a Najeriya, inda ya buƙace su su rage farashin fetur saboda saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *