A ranar Alhamis, Shugaba Donald Trump ya caccaki kuri’ar da aka kada a majalisar wakilan Amurka da ke neman bayar da umarnin janye sojojin Amurka daga Iran.
Yana mai cewa, matakin da ‘Yan Majalisar ke kokarin dauka tsantsar rashin kishin kasa ne da ka iya dakile tattaunawar da Amurkan keyi da Tehran.
Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce“wa zai yi irin wannan abu na rashin kishin kasa? Bayan sun san inda tattaunawar ta tsaya.”
Har ila yau, wasu ‘yan majalisa hudu daga jam’iyyar Trump ta Republican, sun hada kai da ‘yan Democrat a ranar Laraba don goyon bayan kudirin, da ya samu kuri’a 215-208, kuma yanzu haka zaa mika shi gaban zauren Majalisar Dattawa.
-
Yadda muka kashe ɗan ta’adda mafi haɗari ga duniya a Najeriya –Amurka
-
Taƙaddama ta kaure tsakanin Iran da Haddiyar Daular Larabawa a taron BRICS
‘Yan Democrat na zargin Trump da karya kundin tsarin mulki ta hanyar kaddamar da hare-hare kan Iran tare da Isra’ila a karshen Watan Fabarairun shekarar 2026, ba tare da amincewar Majalisar ba.
“‘Yan Democrat sun fi son ganin Amurka ta fadi, maimakon su kalli irin nasorori data samu masu tarin yawa.” Inji Trump