Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 38.66 da kadarori a wani bincike da take gudanarwa kan zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatun man fetur na gwamnati.
Hukumar ta ce akwai yiwuwar wasu tsofaffi da masu riƙe da muƙamai a Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) da wasu ‘yan kwangila za su fuskanci shari’a.
Binciken ya shafi kuɗaɗen da suka kai kusan dala biliyan 2.79 da aka kashe tsakanin shekarun 2021 da 2023 domin gyaran matatun mai na Fatakwal, da Warri da Kaduna.
- Minista: Lokpobiri ya ce tabbataccen tsarin dokoki zai ƙara jawo masu zuba jari a Najeriya
- Sojoji sun ceto ɗalibai da malamai 10 da ISWAP ta sace a Jihar Borno
- Bin doka da ƙarfafa amincewar masu zuba jari ne manufarmu – NMDPRA
EFCC ta ce ta kwato Naira biliyan 9.4 da dala miliyan 21.2, baya ga wasu kadarorin ƙasa da ake zargin suna da alaƙa da mutanen da ake bincike.
Rahotanni sun nuna cewa duk da biliyoyin dalolin da aka kashe wajen gyaran matatun mai, ba a samu gagarumin ci gaba a ayyukansu ba. Hakan ya ƙara ƙarfafa zargin cewa an karkatar ko kuma an wawure wani ɓangare mai yawa na kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan.
EFCC ta ce binciken ya kai ga tambayar sama da manyan jami’ai 30 na NNPCL da kuma jami’ai fiye da 50 na kamfanonin da suka karɓi kwangilolin gyaran matatun mai.