INEC ta ba NDC damar ci gaba da gabatar da 'yan takararta

Hukumar INEC ta sake bai wa jam’iyyar NDC damar amfani da shafin tantance ‘yan takara domin saka sunayensu.

Jagoran jam’iyyar, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana hakan a ranar Talata, yana mai cewa hakan ya biyo bayan shigar da ƙarar daukaka hukuncin kotu.

Ya ce an riga da an saka sunansa da na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, zuwa shafin INEC.

Dickson ya ƙara da cewa za a saka sunan mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa bayan kammala cike wasu takardu.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fidda gwani ƙarƙashin kulawar INEC, kuma tana ci gaba da kasancewa halastacciyar jam’iyya.

Ya buƙaci mambobin jam’iyyar akan kada su firgita, yana mai cewa har yanzu akwai isasshen lokaci a jadawalin INEC don kammala rubuta sunayen dukkan ‘yan takararta.

Jam’iyyar NDC ta ce tana ci gaba da neman hakkinta a kotu, tare da jaddada cewa har yanzu tana da cikakken matsayi na doka har sai an yanke hukunci na ƙarshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *