Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta yanke bai soke rajistar jam’iyyar ba, duk da cewa kotun ta jingine hukuncin da ta yanke a watan Disamban 2025 wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa NDC, ta yi wa jam’iyyar rajista.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Moses Cleopas Zuwoghe, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce tun bayan samun rajista daga hukumar INEC ta fara gudanar da harkokin siyasa da rajistar mambobi da tarukan jam’iyya daga matakin mazabu zuwa ƙasa, tare da gudanar da zaɓen fidda gwani bisa jadawalin INEC.
Sanarwar ta ce ƙungiyar PMP da ta shigar da ƙarar ba jam’iyyar siyasa ce mai rajista ba, kuma ba ta da alaƙa da tsarin rajistar jam’iyyun siyasa da ake gudanarwa yanzu.
- Kotu ta soke rajistar jam’iyyar NDC
- Ƙungiyar Musulmi ta bukaci a sauke farashin mai zuwa ƙasa da N700 a kowace lita
NDC ta ce abin mamaki ne yadda kotun ta amince jam’iyyar PMP na da hurumin shigar da irin wannan ƙara bayan an riga an yanke hukunci na ƙarshe a shari’ar da ta shafi rajistar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa babu wani umarni kai tsaye daga kotun da ke nuna an soke rajistarta, amma ta bayyana rashin gamsuwa da matakin da kotun ta ɗauka, tana mai cewa ta umarci tawagar lauyoyinta da su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin kalubalantar hukuncin.
NDC ta kuma tabbatar wa ‘yan takararta a matakai daban-daban cewa dukkan zaɓukan fidda gwani da ta gudanar da kuma sunayen ‘yan takarar da aka tsayar har yanzu suna nan daram, tana mai jaddada cewa jam’iyyar na ci gaba da kasancewa cikin tsarin siyasar ƙasa.
Jam’iyyar ta yi Allah wadai da duk wani yunkuri na amfani da bangaren shari’a domin takaita tasirin dimokuraɗiyya ko hana jam’iyyun adawa damar shiga zaɓen shekarar 2027, tana mai cewa za ta ci gaba da neman adalci har sai an warware lamarin a kotu