Ƙungiyar Musulmi ta Muslim Media Watch Group of Nigeria (MMWG), ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tilasta wa dillalan man fetur su saukar da farashin mai.
A cewar ƙungiyar, babu “wani dalili” da zai sa a ci gaba da sayar da fetur sama da N1,000 a lita yanzu da farashin ɗanyen mai na duniya ya koma matakin da ya kasance kafin yaƙi.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a wadda ko’odinetan ƙungiyar na kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya rattaba hannu a kai, ƙungiyar ta ce sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka ta rage tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya kuma ta sa farashin ɗanyen mai na duniya ya faɗi.
-
Zulum ya rufe sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a Jihar Borno
-
Ƙungiyar da za ta lashe gasar NPFL mai zuwa za ta karɓi kyautar kuɗi naira biiyan 1
Ƙungiyar ta ƙara da cewa rahotanni sun nuna wasu ƙasashen da yaƙin ya shafa tuni suka riga suka fara samun ragin farashin mai, inda ta yi mamakin dalilin da ya sa hakan bai faru a Najeriya ba tukuna.
Domin sauƙaƙa wahala, ƙungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ba dillalan mai umarnin su dawo da “farashin N700 a lita na fetur kafin yaƙi.”