Zulum ya ce wasu na komawa sansanin IDPs don karɓar tallafi duk da suna da Gidaje

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Bama, sansani mafi girma a Jihar.

Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wata ziyarar tantance halin da ake ciki a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gwoza.

Ya ce bayan kammala tantance ‘yan gudun hijirar Bama, nan da makonni Biyu zuwa Uku za’a rufe sansanin ‘yan gudun Hijira na Gwoza.

Gwamnan ya bayyana cewa an samu nasarar yin hakan ne sakamakon zaman lafiya da ya fara dawowa a yawancin yankunan da mayaƙan Boko Haram suka mamaye a baya.

Gwamnatin jihar ta riga da ta bada mazauni ma al’umma a garuruwa da dama na ƙaramar hukumar Bama da sauran sassan jihar cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Sai dai Zulum ya nuna damuwa kan yadda aikata laifuka ke ƙaruwa a sansanonin, ya ce gwamnatin jihar ba za ta ci gaba da kula da sansanonin ba a irin wannan yanayi.

Yana mai jaddada cewa za a mayar da duk waɗanda aka tantance zuwa garuruwan su tare da haɗin gwiwar shugabannin al’ummomin domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Hukumomi a jihar na cewa binciken da suka gudanar,  na nuni da cewa wasu mayaƙan Boko Haram da ISWAP na ƙoƙarin kutsawa, yayin da wasu mutane dake zaune a gidajen su ke kokarin shiga, domin karbar tallafin ƙungiyoyin agaji ke rabawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *