Gwamnatin Jihar Borno ta sake haɗa tsofaffin ‘yan tawaye su 3,762 da iyalansu cikin al’umma a ƙarƙashin shirin samar da zaman lafiya ta hanyar sulhu da gyaran hali wanda aka fi sani da “Tsarin Borno” (Borno Model).
Wadanda suka ci gajiyar shirin sun haɗa da maza 720, mata 992 da yara 2,050, waɗanda suka miƙa wuya da kansu kuma aka sanya su cikin rukuni na tara, na waɗanda ake yiwa kallon ba su da haɗari ga tsaro.
Gwamnatin jihar ta ce shirin, wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar sake haɗa waɗanda suka tuba daga cikin ‘yan tawaye da suka miƙa wuya.
- Ranar Demokaradiyya: Tunubu ya karrama wasu fitattun yan Kasa
- ‘Yan Sanda sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su a Katsina
- Gobara ta tashi a wata kasuwa dake Kano
Da yake jawabi a wajen taron, Mai Ba Gwamna Zulum Shawara kan Harkokin Tsaro, Birgediya Janar Abdullahi Ishaq mai ritaya, ya bayyana shirin a matsayin wani ɓangare na dabarun gwamnati, ta amfani da hanyoyin zaman lafiya wajen magance matsalar ta’addanci.
Ya ce mahalarta shirin sun samu horo na musamman da ya haɗa da karatun addini, shawarwari kan gyaran hali, tsafta, wayar da kai game da illar miyagun ƙwayoyi da kuma koyon sana’o’i.
Da yawan tubabbun sun koyi sana’ar ɗinki, kafinta, Walda, Gyaran wayoyin hannu, girka na’urorin hasken rana da sauran sana’o’in fasaha.
Yayin da mata suka samu horo kan yin sabulu, saƙa, ayyukan girki da ɗinki, tare da basu kayan fara sana’a domin tallafa musu wajen komawa rayuwa cikin al’umma.
Ishaq ya bayyana cewa sama da mutum 9,600 ne aka maida cikin al’umma tun bayan ƙaddamar da shirin a watan Yulin shekarar 2021.
Sun fito daga ƙananan hukumomin Bama, Gwoza, Damboa, Mafa, Dikwa, Marte, Monguno da Kukawa.
