Wata gobara ta tashi a daren ranar Alhamis, a kasuwar kinswai dake kan titin Murtala Mohammed a karamar hukumar Fagge ta Jihar Kano.
Rahotanni daga Kano na nuni da cewa annobar, ta jawo asarar dukiya mai yawa, yayin da ta bazu zuwa makotan shaguna da Ofisoshi da ke makotaka.
Tuni Hukumar kashe Gobara ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a ta Jihar Kano, (ACFO) Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Jumma’a.
Sanarwar tace Hukumar su ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:54 na daren ranar Alhamis, daga wani ma’aikacin ta, (HFS) Ibrahim Sabo, game da gobarar.
-
An shiga jimami a Jami’ar Kebbi
- Gasar Cin Kofin Duniya: Me ya sa Nahiyar Afirka ta juya wa Afirka Ta Kudu baya?
Hukumar tace ta tarar da wani gini mai bene daya, da wani wurin kasuwanci da ke makwabtaka da shi mai girman kusan kafa 200 zuwa 300, suna cin wuta, Inda tayi kira ga Al’umma su dinga sanar da ita lamari irin wannan akan lokaci.
“Muna kira ga jama’a da su sanar da hukumar kashe gobara nan take duk lokacin da gobara ta tashi. Bayar da rahoto da wuri yana taimakawa wajen rage barnar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi,” in ji sanarwar.
Kawo yanzu, ana cigaba da kididdigar asarar da annobar ta jawo, koda yake babu rahoton asarar rai.
Ko a kwanakin baya sai da kasuwannin Sabon gari da Singa suka tsinci kai a cikin ibtila’in gobara, lamarin da masharhanta ke ganin akwai bukatar sake duba taswirar yadda kasuwannin Birnin suke, domin daukar matakan kariya.
