Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta rattaɓa hannu a kan dokar haramta auran jinsi ko kuma mu’amalar jinsi guda
Gwamnatin dai ta tanadi hukuncin ɗauri da ka iya kai wa shekaru 20 a kan duk wanda aka samu da laifin yin haka.
A ƙarƙashin sabuwar dokar, alkali na iya ɗaure wanda aka samu da laifi daga shekaru biyar zuwa 10 tare da zabin tara ba.
- Zamu sanya kafar wando da kasar Cuba idan ta sayi karin makamai – Hegseth
- Mexico ta doke Afirka ta Kudu
- Birnin Yamai ya kasance kan gaba wajen yawaitar hadurra-Hukumomi
Har ila yau, dokar ta tanadi irin wannan hukunci a kan duk wanda aka samu da laifin sanya hannu ko ɗaukar nauyin aure, shiga ko daure gindi, ko wata ƙungiyar dake alaka da auren jinsi.
Ministan Shari’a na Jamhuriyar Nijar Alio Daouda ya ce an kafa dokar ne bisa cikakken ikon kasar da kuma la’akari da dabi’u da al’adun al’ummar Nijar.
Nijar ta bi sahun wasu kasashen Yammacin Afirka da suka kara tsaurara dokoki kan hulda tsakanin masu jinsi daya a shekarun baya-bayan nan.
