Mexico ta bude gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2026 da kafar dama bayan doke Afirka ta Kudu da ci 2-0, inda kwallayen Julian Quiñones da Raúl Jiménez suka zura kwallayen
Alkalin wasan ya raba jan kati guda Uku, inda Afirka ta Kudu ta kammala wasan da ƴan wasa tara bayan an kori biyu daga cikinsu, yayin da aka kori ɗan wasa daya daga Mexico.
Nasarar ta baiwa ƙasar Mexico maki uku da kuma kwarin gwiwa game da burinsu na fitowa daga rukunin su.
Sai dai Afirka ta Kudu, za ta bukaci ta farfado cikin gaggawa tare da inganta tsarin wasanta kafin wasa na gaba.
Mexico ta hau kan teburin Rukunin ‘A’ bayan lashe wasan bude gasar, yayin da Afirka ta Kudu ta fado kasa bayan rashin nasara a wasan.