Gwamnatin Tarayyar Somaliya ta bayyana takaicinta kan matakin da Amurka ta ɗauka na hana fitaccen alkalin wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar, Omar Abdulkadir Artan, shiga ƙasar.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Somaliya ta fitar, ta ce Artan, wanda ya lashe kyautar Gwarzon Alkalin Hukumar Kwallon Ƙafar Afirka (CAF) ta shekarar 2025, na daga cikin mutanen da suka ɗaga martabar Somaliya a idon duniya.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Somaliya ta yi duk mai yiwuwa ta fuskar hulɗar diflomasiyya domin tallafa wa tafiyarsa, amma ƙoƙarin bai kai ga sakamakon da ake fata ba.
Gwamnatin ta ce tana alfahari da nasarorin da Artan ya samu, tana mai bayyana shi a matsayin abin koyi ga matasan ƙasar da kuma shaidar ƙwazo, jajircewa da sadaukarwa na iya kai mutum ga babban matsayi a duniya.
Somaliya ta kuma tabbatar da cewa Artan ya dawo gida lafiya, kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na ƙasa da ƙasa cikin ƙwarewa da jajircewa kamar yadda ya saba.