Tawagar ’yan mata ’yan kasa da shekara 17 ta Najeriya, Flamingos, za ta koma sansani ranar 14 ga Yuni, yayin da shirye-shirye ke kara kankama don wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta mata ’yan kasa da shekara 17 da za su buga da Jamhuriyar Benin.

Tawagar za ta ci gaba da atisaye a Cibiyar Wasanni ta Remo Stars da ke Ikenne bayan gajeren hutu da ta yi, biyo bayan rawar gani da ta taka akan kasar Guinea.

Karkashin jagorancin koci Hakeem Busari, Flamingos sun samu gurbi a zagaye na karshe, inda suka doke Guinea da jimillar kwallaye 11-0.

Yayinda ta ke daf da samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta mata ’yan kasa da shekara 17, yanzu haka, flamingos ta mayar da hankali ne kan kan Jamhuriyar Benin, wadda ka iya zama mata cikas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *