SPT_GCK_270915_Football league cup Stoke City v Chelsea, Picture Graham Chadwick. Jose Mourinho during the first half

A ranar Talata, Benfica ta raba gari da koci Jose Mourinho, wanda ke kusa da komawa Real Madrid, kuma ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniya da kocin Fulham Marco Silva don maye gurbinsa.

Kungiyar ta Lisbon ta ce Real Madrid ta “tabbatar da aniyarta na daukar Mourinho kan kudi Yuro Miliyan” a cikin wata sanarwa da ta aika wa hukumar kula da kasuwannin hada-hadar kudi ta Portugal.

Daga bisani Benfica ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniyar shekaru biyu da Silva, wanda ya bar Fulham makon jiya bayan shekaru biyar a kungiyar dake buga gasar firimiyar Ingila.

Sake zaben Florentino Perez a matsayin shugaban Real Madrid a karshen mako ya share fagen komawar Mourinho zuwa babban birnin Spaniya.

Mourinho, mai shekara 63, ya taba zama kocin Real Madrid a 2010, inda ya shafe shekaru uku a kungiyar.

A lokacin zamansa, ya lashe La Liga guda daya, Copa del Rey guda daya da kuma Spanish Super Cup a wani yanayi na hamayya mai zafi da Barcelona ta Pep Guardiola.

Real Madrid ta tabbatar da tafiyar koci Alvaro Arbeloa a baya ranar Talata.

Arbeloa, wanda ya zo kungiyar a watan Janairu don maye gurbin Xabi Alonso, ya sanar a watan da ya gabata cewa zai bar mukaminsa a karshen kakar wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *