Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Dattawa ya bayar da umarnin kama tsohon Shuganan Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari.
Kwamitin ya ba da umurnin ne biyo bayan rashin bayyanar Kyari gabansa domin bayar da ba’asin inda Naira Tiriliyan 210 ta shiga, daga shekarar 2017 zuwa 2023.
A yayin zaman, wasu Sanatoci sun roki shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo, da ya sake baiwa Kyari wata damar ko zai bayyana, bisa hujjar cewa yana karbar magani a Jamus.
Sai dai rokon ya fuskanci adawa mai karfi daga wasu mambobin kwamitin, wadanda suka nace a ba da takardar kama tsohon shugaban na NNPCL.
Da yake bayyana matsayin kwamitin, Dankwambo ya umarci a kama Kyari duk inda yake a kawo shi gaban kwamitin.
Da yake jagorantar masu adawa, Sanata Abdul Ningi ya ce ba’asin da baki kan rashin zuwan Kyari gaban kwamiti bai zai wadatar ba, har sai an hada da takardar shaidar shan magani daga likita a rubuce.