Kasashe 11 ne daga cikin 13 da suka fara buga wasan shekaru 96 da suka wuce suka samu nasarar zuwa gasar a kakar bana

An fara gasar cin kofin duniya ne a shekarar  1930, Shekaru 96 da suka gabata, a kasar Uruguay.

Kasashe (13) ne suka fafata a gasar, guda 7 daga kudancin Amurka da suka hadar da Uruguay mai masaukin baki, Sai Ajantina da tazo ta biyu, Brazil, Bolivia, Chile, Paraguay da Peru.

Sai Nahiyar Turai dake da wakilcin kasashe 4 da suka hadar da Faransa, Belgium, Romania da Yugoslavia. Yayin da kasashen Amurka da Mexico ke wakiltar Arewa.

An buga wasannin farko guda biyu a lokaci guda, ranar 13 ga Yulin Shekarar 1930 inda Faransa ta doke Mexico da ci 4–1, ita kuma Amurka ta doke Belgium da ci 3 da nema.

Dan wasan Faransa, Lucien Laurent ne ya fara kafa tarihi a matsayin mutum na farko da ya zura kwallo a raga, a wasan mai masaukin baki Uruguay ta dauki kofin bayan lallasa Ajantina da ci 4 da 2 a wasan karshe.

Daga cikin kasashe 13 da suka fara buga gasar a shekarar 1930, kasashe 11 ne suka samu nasarar fitowa a bana. Yayin da Kasashen Bolivia da Yugoslavia ba su samu gurbin shiga ba.

Gasar ita ce karo na 23 inda a karon farko kasashe 48 suke fafatawa, sabanin kasashe 32 da suka saba bugawa a shekarun baya.

Babban abinda ya banbanta gasar ta bana da sauran wadanda akayi a baya shine mika bakuncin ta ga kasashe  Uku a lokaci guda.

Sannan jimillar kasashe  Bakwai ne suka zabi kafa sansanin atisayen su da masaukansu a cikin kasar Mexico, daga farko zuwa karshen  gasar, maimakon zama a Amurka.

Mexico mai masaukin baki da Afirka ta Kudu da Uruguay. Sauran sun hadar da Koriya ta Kudu  da Tunisiya da Colombia da kuma Iran, wacce ta kafa sansaninta a birnin Tijuana dake Arewa maso Yammacin Mexico.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *