Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yaƙin da take yi da masu garkuwa da mutane, inda ta ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su.
Da yake gabatar da rahoton nasarorin da rundunar ta samu a hedikwatar ta da ke Katsina, Kakakin Rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an kama mutane 225 da ake zargi da hannu a laifuka daban-daban.
Waɗanda aka kama sun haɗa da mutane 7 da ake zargi da garkuwa da mutane, 10 masu fashi da makami, ɗan bindiga guda ɗaya, masu ba da bayanai ga masu laifi guda 2, da masu safarar miyagun ƙwayoyi guda 21.
- ‘Yan Sanda sun kwato makamai a Kano
- IGP Disu: Mun haramta tuka Motoci da ake rufe musu Lamba a Najeriya
- Da Dumi-Dumi: An harbe ’yan bindiga a Abuja
Haka kuma, rundunar ta kama mutane 10 da ake zargi da kisan kai, mutane 36 da ake zargi da laifukan fyade da luwadi, mutane 13 da ake zargi da tayar da tarzoma, da wasu mutane 130 bisa wasu laifuka daban-daban.
Bugu da ƙari, an kwato dabbobi 466 da ake zargin an sace, motoci 3, babura 22, buhuna 4 na wayoyin lantarki da aka lalata, da kuma tarin miyagun ƙwayoyi, tare da ganyen da ake zargin tabar Wiwi ce.
DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce rundunar ta ƙaddamar da sabon sashen yaƙi da munanan laifuka mai suna Violent Crime Response Unit (VCRU), tare da ƙarfafa ayyukan tattara bayanan sirri da sintiri a sassa daban-daban na jihar.
Rundunar ta kuma buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro, domin ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
