Kwamishinan ya bukaci jama'a su kai rahoton duk wanda suka gani dauke da raunin harbin bindiga

‘Yan Sanda sun harbe ’yan bindiga biyu daga cikin gungun da ake kyautata zaton suke addabar mazauna Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya, CP Ahmed Mohammed Sanusi, ya bayyana hakan ga manema labarai a shelkwatar rundunar ranar Laraba, ya ce shi ne ya jagoranci aikin da kansa.

CP Ahmed yace sun gudanar da wani sumame a Yankin Bhyazin, bayan sace wasu mazaunan sa biyar a unguwar Paze a makon jiya, yankin dake karkashin Karamar Hukumar Bwari.

A cewar kwamishinan ’yan sandan, sun ceto wadanda aka sace din, yayin da aka cafke wasu ‘yan bindiga wadanda aka bayyana sunansu da Icheh Mohammadu da Abubakar Usman, yayin da sauran suka arce.

“Yayin sumamen, mun kwato bindigogi kirar AK-47 guda Biyu da kwanson harsashi, yayin da aka kama  Biyu daga cikin ‘yan ta’addar yayin musayar wuta,” in ji shi.

CP Sanusi ya ce an kai mutum biyar da aka ceto asibiti, dominn samun kulawa, kafin mayar dasu ga iyalansu.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya, asibitoci masu zaman kansu da na gwamnati da kuma al’umma da su gaggauta kai rahoton duk wani mutum da ya zo da raunin harbi ko neman magani a wajen su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *