Amurka na tsanantsa tsaro ne a saman ruwan domin gurgunta kasar Iran daga fito

Matuƙan jiragen ruwa uku ‘yan ƙasar Indiya sun mutu a hare-haren da aka kai kan wasu jiragen kasuwanci uku a Mashigin Hormuz a wannan makon.

yayin da Amurka ke ƙara tsaurara matakan killace tashoshin jiragen ruwa na Iran ta hanyar rundunar ruwanta.

A ranar Laraba, gwamnatin India ta gayyaci wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka a Babban Birnin kasar New Delhi, domin neman ba’asi game da wani harin sojin Amurka, kan wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar Palau a gabar tekun Oman.

Sa’o’i kaɗan kafin hakan, Amurka ta kuma kai hari kan wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar Palau wanda ke ɗauke da matuƙan Indiya 24 a kusa da gabar tekun Oman.

A ranar Alhamis, Rundunar Amurka (CENTCOM) ta bayyana cewa dakarunta sun “nakasta” wata tankar ɗaukar mai a Tekun Oman, bayan matuka jirgin sun karya dokar killace Iran ta hanyar ƙoƙarin jigilar Mai.

Zuwa safiyar Juma’a, Shugaban Amurka Donald Trump da jami’an Iran sun nuna kyakkyawan fata game da yiwuwar cimma yarjejeniyar tsawaita tsagaita wuta, wadda aka bude tattaunawa a cikin watan Afrilu a kasar Pakistan.

Sai dai ga dubban ma’aikatan jiragen ruwa da suka makale a bangarorin biyu na Mashigin Hormuz, na cewa zaman lafiya har yanzu yana da nisa.

Hare-haren da aka kai kan jiragen da ke ɗauke da matuƙan Indiya sun bude sabon tushen takun saƙa tsakanin Washington da New Delhi,, dangantakar da ta ƙara tsami a wa’adi na biyu na Shugaba Trump.

Ana sa ran Trump zai gana da Firaministan Indiya Narendra Modi a mako mai zuwa yayin taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G7 da za a gudanar a Faransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *