Gwamnatin Tarayya ta ce shirye-shirye sun yi nisa a yunkurin mayar da Abuja cibiyar kudin bai-daya na Afirka ta hanyar karbar bakuncin Cibiyar Kudi ta Afirka (AMI).
Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun Shugabar Sashen Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Misis Efe Ovuakpori.
Sanarwar, wadda ta ce wakilan Najeriya sun gabatar da hujjoji game da cancantar birnin na Abuja a wajen wani babban taron Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a Washington, ta kara da cewa tuni yunkurin ya tashi daga bayyana aniya zuwa daukar kwararan matakai.
- Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin bana
- Minista ya roki masu kamfanonin jiragen sama da kada su daina aiki
- Kotu ta bai wa EFCC umarnin kamo Sadiya Umar Farouq
Da yake jawabi a wurin taron a madadin Ministan Kudi Wale Edun, Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Mista Raymond Omachi, ya ce tuni Najeriya ta baza kafaciti.
“Mun riga mun wuce matakin bayyana manufa; muna nan muna kakkafa abubuwan da ake bukata don tallafa wa cibiyar, kuma Najeriya a shirye take ta sauke nauyin da yake kanta”, inji Mista Omachi.
‘Ofis ya samu’
Shi ma a nasa jawabin a madadin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Yemi Cardoso, Mataimakin Gwamna Mai Kula da Manufofin Tattalin Arziki, Dokta Muhammad Sani Abdullahi, ya ce tuni aka samar da ofis a Abuja don amfanin cibiyar.
“An samar da wani gini na musamman [don amfanin cibiyar] wanda za a iya zuwa a duba.
“Wannan ya nuna cewa a shirye muke mu dauki nauyin kasancewa mai masaukin cibiyar”, inji shi.
AMI wata sabuwar ciniya ce da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta kirkiro da nufin aiki don tabbatar da hadewar kasashen nahiyar ta fuskar manufofin kudi, wadda a karshe za ta kai ga samar da kudin bai-daya.
A watan Satumba na 2026 ake sa ran kaddamar da cibiyar a hukumance.
Wannan yunkuri na Najeriya dai yana zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta umaeci ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke Abuja wadanda ayyukansu ba su wajaba su fice daga birnin tana kafa hujja da karuwar matsalar tsaro.
