Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon gadar musayar hanya (interchange) da kemahaɗar hanyar Arterial Road N16 da Ring Road II, wadda ke haɗa yankin Jahi da Gwarimpa a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Alhamis 25/6/2026.
Minista a babban birnin tarayya abuja Dakta Mariya Mahmood Bunkure ta bayyana aikin a matsayin muhimmin ci gaban ababen more rayuwa da zai inganta haɗin kai tsakanin yankuna daban-daban na birnin, tare da sauƙaƙa zirga-zirga da rage cunkoso a hanyoyi.
- Ba mu kai ‘yan bindiga aikin Hajji ba – Gwamnatin Katsina
- Gwamnatin Tarayya ta gano tarin ma’adanai masu daraja a Jihar Kaduna
- EFCC ta kama mutane 17 da ake zargi da damfara ta yanar gizo
A cewarta, wannan aikin zai taimaka wajen inganta harkokin tattalin arziƙi a Abuja, rage lokacin tafiya tsakanin yankuna, tare da sauƙaƙa jigilar mutane da kaya zuwa cibiyoyin kasuwanci..
Haka kuma, Mariya ta bayyana cewa aikin yana daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙarƙashin shirin sabunta fata, wanda ke mayar da hankali kan samar da ababen more rayuwa da ke shafar rayuwar ‘yan ƙasa kai-tsaye.
Ana saran sabon titin zai taimaka wajen haɗa al’umma da dama, ƙarfafa kasuwanci, tare da tallafa wa ci gaban da Babban Birnin Tarayya ke fuskanta sakamakon ƙaruwa da yawan jama’a.
