Wata kotu a babban birmin Tarayya Abuja ta yankewa waniai suna Jonathan Marcus humuncin kisa ta hanyar rataya, bisa samunsa da laifin yin garkuwa tare da hallaka wasu ma’aurata.
Rundunar ‘Yan Sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta bayyana cewa ta samu nasarar danke Jonathan, wanda aka gurfanar bisa zargin kashe Mista Adebola Ezekiel (80) da matarsa, Misis Abiodun Ezekiel, a yankin Apo Legislative Quarters, Abuja, a ranar 1 ga Afrilu, 2024.
Bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda sun fara bincike, wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin, wanda ya taɓa aiki a matsayin direban mamatan.
- INEC da NOA sun ƙarfafa wayar da kan Jama’a kan Zaɓe
- Babban Bankin bada ƙananan lamuni 46 da CBN ya soke akwai guda 14 a jihar Kano
- NCDC ta ƙarfafa shirinta na dakile cutar Ebola a Nijeriya
An gano cewa Jonathan ya tsere zuwa Obajana a Jihar Kogi bayan aikata laifin, inda daga baya aka kama shi aka dawo da shi Abuja domin ci gaba da bincike.
A yayin bincike, an ce wanda ake zargin ya amsa laifi na shiga gidan mamatan da misalin karfe 11:00 na dare a ranar da lamarin ya faru, inda ya aikata kisan.
Bincike ya kuma nuna cewa an kore shi daga aiki a baya sakamakon sabani da mamatan.
Daga bisani an gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun FCT, inda kotu ta tabbatar da laifinsa ba tare da shakka ba.
Mai shari’a M. S. Idris ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.