Cibiyar Kula da Cututtuka da Kare Aukuwarsu ta Nijeriya (NCDC) ta ce ta ƙara ƙarfafa shirye-shiryenta na dakile yiwuwar ɓarkewar cutar Ebola a ƙasar, bayan ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Yaƙi da Cutar Ebola.
Darakta Janar na Hukumar, Dr. Jide Idris, ya jagoranci tarurrukan wasu ƙananan kwamitoci da ke da alhakin sa ido kan cututtuka, gwaje-gwaje, kula da marasa lafiya, da kuma samar da kayan aiki domin tunkarar barazanar cutar.
NCDC ta ce tarurrukan sun mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, inganta tsarin gano masu ɗauke da cutar da wuri, shirya dakunan gwaje-gwaje, kula da masu kamuwa da cutar, tattara kayan aiki da kuma tura ƙwararrun ma’aikata domin tabbatar da cikakken shiri.
Hukumar ta bayyana cewa matakan sun zama wajibi ne sakamakon ci gaba da ɓarkewar cutar Ebola a ƙasashen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Uganda, domin hana yiwuwar bazuwar ta zuwa Nijeriya.
Taron ya samu halartar wakilai daga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, NCDC, Hukumar Kula da Lafiya a kan iyakoki, Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran hukumomi da ƙungiyoyin da ke da ruwa da tsaki a fannin lafiya.
