Babban Bankin Najeriya ya soke lasisin ƙananan Bankunan bada lamanin kuɗaɗe guda 14 a Kano, da 8 a Legas da 26 a sauran jihohi.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin gudanarwa na bankunan lamani guda 46 daga 1 ga Yulin 2026, wanda 14 daga ciki a jihar Kano suke.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Laraba, Gwamnan CBN, Mista Olayemi Cardoso, ne ya amince da ɗaukar matakin bayan bankunan sun kasa cika ƙa’idojin da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da aiki a matsayin cibiyoyin kuɗi masu lasisi.
-
Dillalan Man Fetur sun yi barazanar rufe gidajen mai idan…
-
Zamfara ta ƙaddamar da cibiyar samar da ruwa sha
CBN ya bayyana cewa an soke lasisin bankunan ne saboda dalilai da suka haɗa da rashin isassun kadarori da za su biya basussukan da ke kansu.
Bankunan sun dakatar da ayyukansu ba tare da amincewar babban bankin ba, da kuma dakatar da gudanar da harkokin kuɗi, da gaza fara aiki cikin watanni 12 bayan samun lasisi, da kuma kasa riƙe mafi ƙarancin jarin da doka ta tanada ba.
Bankin ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da daidaito da kwanciyar hankalin masu zuba jari, a tsarin kuɗi na ƙasar.
Hakan zai kare kuɗaɗen masu ajiya, tare da tabbatar da cewa cibiyoyin kuɗi masu lasisi suna bin dokoki da ƙa’idojin da ke aiki.