Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da aiwatar da ayyukan tituna 27 da kuɗinsu ya haura Naira tiriliyan 3.9 a jihohi 15 na ƙasar nan, a wani yunƙuri na inganta hanyoyin sufuri da bunƙasa ababen more rayuwa.
Ministan Ayyuka, David Umahi, ne ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce ayyukan za su gudana a jihohin Adamawa da Benue da Cross River da Ebonyi da Ekiti da Kogi da Kwara da Lagos da Niger da Ondo da Osun da Oyo da Plateau da Taraba da kuma Yobe.
- EFCC ta ƙwato sama da Naira biliyan 38 a binciken kuɗaɗen gyaran matatun mai
- Sojoji sun ceto ɗalibai da malamai 10 da ISWAP ta sace a Jihar Borno
Umahi ya ce daga cikin manyan ayyukan da aka amince da su akwai sake bayar da kwangilar hanyar kilomita 409 mai layi biyu a Jihar Niger ƙarƙashin tsarin Tax Credit, wadda ɗan kasuwa Aliko Dangote zai aiwatar kan kuɗin da ya kai Naira tiriliyan 1.8. Sauran sun haɗa da faɗaɗa da sake gina manyan tituna a jihohin Kwara, Oyo, Ebonyi, Kogi, Benue, Cross River, Adamawa da sauran jihohi.
Ministan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da cikakken tsarin ba da aikin kula da babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan ga kamfani mai zaman kansa, tare da ba da umarnin fara sake gina sassan hanyar da suka lalace a yankin Ibadan ta hanyar amfani da siminti.
Haka kuma, Umahi ya sanar da kammala aikin sashe na farko na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano mai tsawon kilomita 118, wanda ya lakume kuɗi kimanin Naira biliyan 137.