Ƙasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun fara aiwatar da matakin ficewarsu daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), kamar yadda kotun ta tabbatar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ICC ta ce ficewar ƙasashe daga kotun na iya raunana ƙoƙarin duniya na tabbatar da adalci da kuma kawo ƙarshen rashin hukunta masu aikata manyan laifuka.
Ƙasashen uku da ke ƙarkashin mulkin sojoji sun fara sanar da kotun aniyarsu ta ficewa tun a watan Satumban bara.
- An ciro Mutumin da ya shafe kwanaki Takwas a ƙarƙashin baraguzan gini a Venezuela
- Cutar Ebola: Shugaban Ramaphosa ya kai ziyarar goyon baya ƙasar Kwango
- Mummunar ambaliyar ruwa ta halaka mutum 12 Accra
Waɗannan ƙasashe uku, waɗanda suka fice daga kungiyar ECOWAS, sun kafa Kawancen Kasashen Sahel (Alliance of Sahel States) a shekarar 2024. Tun daga lokacin suka yanke hulɗa da tsohuwar ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka wato Faransa, da kuma wasu ƙasashen Yamma da dama, inda suka karkata ga amfani da dakarun haya na Rasha domin samun tallafin soja
Yanzu sun fara tsarin janyewa daga Yarjejeniyar Roma (Rome Statute), wadda ta kafa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya. Wannan tsari zai ɗauki shekara guda kafin ya kammala.
Kotun ta ICC, wadda ke da hedikwata a birnin Hague na ƙasar Netherlands, tana gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifukan kisan Ƙare dangi (genocide) da laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaƙi da kuma laifin kai hari kan wata ƙasa, idan kotunan ƙasashensu ba za su iya hukunta su ba.
A lokacin da suka sanar da shirin ficewar tasu, ƙasashen uku na Sahel sun bayyana ICC a matsayin “kayan aikin danniya na sabon mulkin mallaka.”
A halin yanzu, kotun tana da ƙasashe mambobi 125, sai dai wasu manyan ƙasashe irin su China da India da Rasha da Amurka da Isra’ila ba su shiga cikinta ba.