Shugaban ƙasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya gudanar da wata ganawar ƙoli da takwaransa na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango tare da wakilan gwamnatocinsu a birnin Kinshasa.

Ziyarar na daga cikin shirin nuna haɗin kai na Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), inda Shugaba Ramaphosa ke wakiltar matsayinsa na Jakadan Tarayyar Afirka kan Shirye-shirye da rigakafi da martani ga annoba.
Manufar ziyarar ita ce tattaunawa da Shugaba Tshisekedi tare da nuna cikakken goyon bayan tarayyar Afirka a Kudu ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, yayin da ƙasar ke fuskantar sabuwar ɓarkewar cutar ebola.

Haka kuma, tawagar ta tattauna kan yadda za a ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen Afirka domin samar da ingantaccen martani ga annobar tare da ƙara haɗin kai tsakanin ƙasashen da ke maƙwabtaka da Kongo wajen sa ido da shirin daƙile yaɗuwar cutar ta kan iyakoki.

Bugu da ƙari, ziyarar na da nufin jawo ƙarin goyon bayan siyasa da na fasaha da kuma na kuɗi daga ƙasashen mambobin tarayyar Afirka da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin tallafa wa ƙoƙarin daƙile cutar.

Ana sa ran waɗannan matakai za su taimaka wajen shawo kan ɓarkewar Ebola da ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar jama’a da kuma inganta shirye-shiryen tunkarar duk wata annoba da ka iya tasowa a nahiyar Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *