Masu aikin ceto a Venezuela sun ciro wani mutum mai shekaru 43 da rai, bayan ya shafe kwana takwas a ƙarƙashin baraguzan gini da ya rushe sakamakon girgizar ƙasa.
An ciro Hernan Gil ne daga wani gini mai hawa bakwai da ya rushe a babbar tashar ruwa ta Catia La Mar, yamma da babban filin jirgin saman birnin ƙasar.
Masu aikin ceto sun ba shi ruwa tare da sanya masa na’urar daidaita numfashi (oxygen) gabanin wucewa dashi Asibiti.
- Girgizar ƙasa mai ƙarfi ta kashe mutum 32 tare da jikkata ɗaruruwa a Venezuela
- Venezuela: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 235
- Kenya ta tsaurara tsaro yayin da aka cika shekaru biyu da zanga-zangar matasan Gen Z
Sai dai hukumomi sun ce adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa kusan 2,300, yayin da har yanzu ba a gano inda dubban mutanen suke ba.
A dalilin haka ne, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta nemi tallafin Dala Miliyan 50, domin taimaka wa kusan mutane 500,000 da girgizar ƙasar ta shafa.
